in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta yaba da matakin Saudiyya a Yemen domin maido da tsarin mulki a kasar
2015-03-31 10:57:43 cri

Kasar Nijar ta bayyana gamsuwarta a ranar Litinin da matakin da kasar Saudiyya ta dauki jagorancin kawancen dake kai hare hare domin tallafawa hukumomin Yemen a lokacin da suke fuskantar matsalar tashe tashen hankali a dukkan fadin kasar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin da yamma ta gidan talabajin na kasa, kasar Nijar ta bayyana cewa, tana sanya idon kan halin da ake ciki a kasar Yemen, musammnun kan yadda ake kokarin kawo baraka da yunkurin kifar da tsarin demokaradiyya daga wajen 'yan tawayen Houthis.

Kasar Nijar na maraba da matakin Saudiyya bisa jagorantar kawancen da ke hare hare a kasar Yemen bisa taken "guguwar kin nuna sassauci" domin taimakawa halattacciyar gwamnatin kasar Yemen ta yadda za'a maido da zaman lafiya, da murkushe masu tada kayar baya, da kuma maido da tsarin mulki a dukkan fadin kasar Yemen, in ji wannan sanarwa.

Gwamnatin Nijar ta yi kiran gamayyar kasa da kasa, musammun ma kungiyar ci gaban kasashen musulunci, kungiyar kasashen Larabawa da na kwamitin dangantakar yankin Golf da su taimakawa gwamnatin da aka zaba da halatattun hukumomin kasar Yemen.

Tun daga ranar 28 ga watan Maris ne dai kasar Saudiyya take jagorantar aikin soja kan kasar Yemen mai taken "guguwar kin nuna sassauci", tare da kasashen yankin Golf goma tare da ita, da kuma Masar da Jordan, domin fatattakar 'yan tawayen shi'a na Houthis, da suka kori hukumomin kasar daga babban birnin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China