Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei yace Sin tana fatan dukkan bangarorin zasu aiwatar da yarjejeniyar kwamitin sulhun MDD da kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin Gulf wato GCC, su koma kan teburin shawarwari ba tare da bata lokaci ba.
Mr Hong Lei yace hakan zai samar da mafita na siyasa da zai tafi da yanayin da kasar ta Yemen ke ciki tare da kula da dukkan wadanda hakan ya shafa wanda a ganin kasar Sin zai kawo daidaito da ikon a hukumance ga kasar cikin lokaci. Kakakin ya fadi haka ne a tyayin da yake bayani ga manema labarai a laraban nan game da shawarar kasar Saudiya da kawayenta na dakatar da kai harin sama a kasar ta Yeman.(Fatimah Jibril)