A daya hannun kuma, ofisoshin MDD a Yemen, ciki hadda ofishin babban kwamishinan kula da harkokin hakkin bil'adam na MDD a kasar, su ma sun lalace sakamakon harin sama da aka rika kaddamarwa.
Asusun yara na MDD ya tabbatar da cewa, a kalla yara kananan 140 ne aka shigar cikin dakarun soja a Yemen, yayin da aka mamaye makarantu 30, aka kuma kai hari kan asibitoci 23.
Game da wannan batu, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta furta cewa a yanzu haka, dukkanin asibitocin dake Yemen suna fama da karancin magunguna.
Tun dai daga karshen watan Maris din da ya gabata ne hadaddiyar rundunar sojin kawance da kasar Saudiyya ke jagoranta ta fara kai hare-hare ta sama kan sansanonin dakarun Ḥūthi dake kasar ta Yemen, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu kuma suka yi gudun hijira.
Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, a kalla mutane dubu 150 ne suke gudun hijira sakamakon wannan rikici. (Fatima)