Rahotanni daga Aden na kasar Yemen sun tabbatar da cewar, bangaren al-Qaida a kasar ya karbi filin saukan jiragen saman, da ma wani sansanin soji bayan wata bata kashi da suka yi da jami'an tsaro a gundumar Hadramout dake kudu maso gabashin kasar a yammacin Alhamis din nan.
Kamar yadda wani jami'in gwamnati ya tabbatar, 'yan kungiyar ta al-Qaida dauke da manyan makamai sun kai farmaki a kan sansanonin soji da dama da suka hada da na makaman soji na shiyya na 27, suka kwace ikon filin saukan jiragen samanta tare da filin saukan jiragen sama na Rayan dake birnin Mukalla, babban birnin gundumar Hadramout.
Jami'in ya ce, 'yan al-Qaidar dauke da manyan makamai sun riga sun mamaye wannan waje, abin da ya sa dole masu tsaron wajen na gwamnati suka ja baya
Sai dai kamar yadda wani basaraken wannan yankin ya shaida wa Xinhua, jami'an yankin da wakilan kabilu suna tattaunawa da shugabannin al-Qaidar domin su samu a mayar da filin saukan jiragen saman ga hukuma lami lafiya.
Haka kuma jami'an tsaro na wannan waje sun tabbatar wa Xinhua cewa, kazamin fada ya kaure tsakanin jami'an tsaro na soji da na al-Qaidar a sansanin mai na Dhabah dake yankin Shihr na gundumar Hadramout. (Fatimah)