in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kwashe mutanenta daga Yemen
2015-03-31 10:05:25 cri

Kasar Sin na kwashe daruruwan mutanenta a yanzu haka daga kasar Yemen ta hanyar taimakon jiragen yakin kasar Sin, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar madam Hua Chunying a ranar Litinin.

Jami'ar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai cewa, kasar Sin ta shirya kwashe mutanenta 122 dake Yemen domin isar da su zuwa Djibouti, wata kasar Afrika dake kallacin kasar Yemen, a yankin ruwan tekun Aden. Haka kuma, ta kara da cewa, jakadan kasar Sin dake Djibouti ya samar da duk wani taimakon da ya dace ga wadannan Sinawa domin taimaka musu dawowa kasar Sin cikin gajeren lokaci.

Domin kwashe 'yan kasarta, gwamnatin kasar Sin ta ba da umurni a ranar Lahadi ga jiragen ruwan yakinta da ke yaki da 'yan fashin taken a yankin ruwan Golf Aden da Somaliya da su juya zuwa kasar Yemen. Sun ci gaba da tuntubar juna yadda ya kamata tare da bangarorin da abin ya shafa kuma suna iyakacin kokarinsu domin taimakawa sauran mutane 400 dake kasar ta Yemen, ta yadda za'a gudanar da aikin kwashe su cikin tsari da tsaro, in ji madam Hua.

Kasar Yemen dai na fama a yanzu da tashe tashen hankalin siyasa da tafka kazamin yaki tsakanin 'yan tawayen Houthis da sojoji masu biyayya ga shugaba Abd Rabbo Mansour Hadi, da ya tsere daga kasar.

Madam Hua ta kuma nuna godiya ga kasashen Yemen, Djibouti da sauran bangarorin da abin ya shafa game da taimakon da suke ba da wa wajen kwashe Sinawan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China