in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 50 ne suka halaka a sansanin 'yan gudun hijira da ke Aden a Yemen
2015-05-07 10:08:40 cri

Kimanin mutane 50 ne suka halaka, kana wasu 100 suka jikkata, galibinsu mata da kananan yara lokacin da wasu rokokin suka fada kan sansanin 'yan gudun hijira da ke Aden a kudancin kasar Yemen.

Wani jami'in kiwon lafiya da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, lamarin ya faru ne lokacin da 'yan gudun hijirar ke kokarin shiga kwale-kwale don tserewa fadan da ke faruwa a yankin Tawahi.

Rahotanni na cewa, fada ya kaure ne tsakanin mayakan Houthi da mayakan da ke biyayya ga shugaban Yemen Abdu-Rabbu Mansour Hadi a garin Aden da ke yankin Tawahi, lamarin da ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu zuwa gundumar Buraiga da ke yammacin Aden ta kwale-kwale.

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, mayakan na Houthi sun kashe Manjo janar Ali Nasser Hadi, kwamandan runduna ta hudu na sojojin yankin wanda ya ayyana goyon bayansu ga shugaba Hadi a yayin fito na fito da 'yan tawayen a kusa da mashigar garin Aden da ke gundumar Tawahi a ranar Laraba.

Bayanai na cewa, mayakan na Houthi sun kara dannawa zuwa wasu sassan garin Tawahi bayan da suka kwace garuruwa da ke kusa da yankin, lamarin da ya tilastawa dakarun da ke kawance da kasar Saudiya kaddamar da hare-hare ta sama kan gine-ginen da ke hannun 'yan tawayen.

Har yanzu babu wasu hakikanan alkaluma game da barna ko yawan mutanen da suka rasa rayukansu, sakamakon hare-hare ta sama da Saudiya ke jagoranta tun fara wannan yaki a kasar ta Yemen. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China