Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya ja hankulan daukacin sassan dake gwabza fada a kasar Yemen, da su kare rayukan fararen hula, su kuma ba da damar shigar da kayayyakin jin kai cikin kasar.
Ban, ya ce, a wannan gaba da fada ke kara kazanta a kasar, ya zama wajibi ga dukkanin bangarorin kasar su mutunta dokokin kasa da kasa.
Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, halin jin kai na dada tabarbarewa a Yemen, ta yadda al'ummar kasar ke kara fuskantar matsananciyar bukata ta muhimman ababen more rayuwa, da suka hada da ruwan sha, da abinci, da magunguna.
Hakan a cewarsa ya biyo bayan yunkurin da 'yan adawar Houthis da kawayansu suka yi, na kwace iko daga zababbiyar gwamnatin kasar, matakin da ya sabawa kudurorin kwamitin tsaron MDD, da ma manufar wanzar da tsarin dimokaradiyya a kasar.
Ban Ki-moon ya kuma bayyana shawarwari da MDD ke goyon baya, a matsayin hanya daya tilo ta maida Yemen kan turba ta gari, tare da tabbatar da 'yancin kan kasar, da hadin kan al'ummarta.
A wani ci gaban kuma, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, rahotanni daga ofishin kula da ayyukan ba da agajin jin kai na MDD OCHA, na nuna cewa, ayyukan jin kai a kasar ta Yemen na fuskantar babbar barazana, a wannan gaba da yaki ke kara kazanta.
Dujarric ya ce, a wannan lokaci al'ummun kasar musamman mazauna yankunan Aden, da Lahj da Al Dhale'e, na fuskantar matukar matsin lamba a fannin tsaron rayukan su.
A cikin watan da ya gabata ne dai kasar Saudi Arabia ta fara kaddamar da hare-hare ta sama, kan mayakan Houthi a birnin Sana'a, da wasu karin biranen kasar, a wani mataki na tallafawa gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi, wajen murkushe 'yan tawaye masu yunkurin mamaye wasu karin sassan kasar.
MDD dai na ganin ya zama wajibi a komawa matakan siyasa, a matsayin hanyar warware rikicin kasar da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa. (Saminu)