in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya damu da tabarbarewar yanayin jin kai a Yemen
2015-05-01 16:33:14 cri
A jiya ne babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya fidda wata sanarwa dangane da tabarbarewar yanayin jin kai a kasar Yemen, inda ya nuna damuwarsa matuka sabo da ci gaba da yadda ake halaka fararen hulan kasar ta kasa da sama.

Cikin sanarwar, Mr.Ban ya ce, cikin 'yan makwanin nan da suka gabata, mutane sama da dubu daya da dari biyu aka halaka sakamakon rikice-rikice a kasar, yayin da kimanin dubu dari uku suka gudu daga gidajensu, haka kuma, baya ga wasu fararen hulan da ake kaiwa hare-hare ta sama.

Bugu da kari, ana fuskantar matsalar jigilar abinci, magunguna da kayayyakin agaji cikin kasar, yayin da harkokin kiwon lafiya da sadarwa suka lalace. Dangane da lamarin, Mr. Ban ya sake yin kira da bangarorin da rikicin kasar Yemen ya shafa da su tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, da kuma tabbatar da samar da isashen abinci da kayayyakin da ake bukata a yankunan da rikicin ya shafa, ta yadda za a iya magance ci gaban tabarbarewar yanayin jin kai a kasar.

Ban da haka kuma, kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa dake yankin Gulf na GCC ya jaddada a jiya Alhamis cewa, ya kamata a kira taron yin shawarwari don kawo karshen rikicin Yemen da kuma sulhunta bangarorin da rikicin ya shafa a babban birnin kasar Saudiya, watau Riyadh, maimakon wurin da kasar Iran ta ba da shawara a baya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China