A cewar ministan, idan har darajar danyen mai za ta tsaya a dalar Amurka 60 kan ganga guda, kuma kasashen yammacin duniya suka ci gaba da sanya ma kasar Rasha takunkumi, hakan zai sa kasar ta gaza samun rancen kudi daga ketare, kana ta rasa jarin waje cikin kasuwanninta. A wannan yanayi mai tsanani, ana kuma hasashen rasa damar farfado da tattalin arzikin kasar ya zuwa shekarar 2016. Kana ya zuwa wannan lokaci za a fuskanci tafiyar wahainiya game da farfadowar.
A cewar Ulyukaev, ko da za a fuskanci hauhawar farashin kaya, kasar ba za ta sassauta farashin ta hanyar raba kayayyaki ga jama'a ba, domin hakan na iya boye hauhawar farashin, ya kuma hana tattalin arzikin kasar farfadowa.(Bello Wang)