Lavrov ya bayyana hakan ne ga taron manema labaru, bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Latvia Edgars Rinkevics.
Latvia dai ita ce ke jagorantar kungiyar EU a wannan karo.
A cewar ministan harkokin wajen kasar ta Rasha, Moscow na fatan yin hadin gwiwa tare da kungiyar EU bisa tushen adalci da cimma moriyar juna, don haka bai kamata a dauki matsaya biyu yayin da ake gudanar da harkoki da ita ba. Lavrov ya jaddada cewa, takunkumin da ake sanyawa kasar Rasha a yanzu haka ya sabawa doka.
Kaza lika Mr. Lavrov ya bayyana cewa, yunkurin da ake yi na gudanar da hadin gwiwa a sauran fannoni ba zai yi wata fa'ida ba, muddin dai ba a warware matsalar Ukraine ba. Don haka ya ce ya kamata kasashe yammacin duniya su gaggauta fara aiwatar da hadin gwiwa tare da kasar Rasha, a fannin yaki da ta'addanci. (Zainab)