in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare na samun babban ci gaba
2015-04-08 10:42:49 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce manufar raya gabashin kasa da Rasha ta tsara, da ta gaggauta habaka yammacin kasa da Sin ta tsara, sun kawo babbar dama ga kasashen biyu wajen inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu.

Mr. Wang wanda ya bayyana hakan a jiya Talata a birnin Moscow, yayin wani taron manema labaru da suka gabatar shi da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, ya kara da cewa dangantakar hadin gwiwa ta moriyar juna tsakanin sassan biyu ta zamo wani abun misali a fannin raya sabon nau'in dangantakar kasa da kasa a duniya, kuma ya kamata kasashen biyu su yi hobbasa wajen wanzar da dawaumammen zaman lafiya a duniya.

Wang Yi ya ce, Rasha babbar kasa ce da ke ketare nahiyoyin Asiya da Turai. Kuma cikin 'yan shekarun nan, yayin da Rasha ta fidda manufar raya yankin gabashin kasa, kasar Sin ita ma, ta nacewa bin manufar bude kofa ga kasashen waje, kuma ta gaggauta raya yankin yammacinta, wanda hakan ya kawo babbar dama ta hada manufofin kasashen biyu tare.

Ya ce, kamata ya yi a hada manufar raya hanyar Siliki ta Sin, da bunkasa hanyoyin ketaren nahiyoyin Turai da Asiya, da gaggauta raya yankin gabashin kasar Rasha bai daya. Irin matakan da suka dace a dauka, sun kunshi inganta mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya. Hakan a cewarsa, baya ga kawo sabbin abubuwa na raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu, zai kuma haifar da sabbin fannonin habakar hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu, da bunkasa raya nahiyoyin Asiya da Turai.

Wang Yi ya kuma kara da cewa, duk da cewa kasashen biyu ba su da wani kawance na daban, a daya hannun kuma ba sa yaki da juna, kana suna habaka raya dangantakar su ba tare da nufin muzgunawa wata kasa ta daban ba. Kasashen biyu na mai da hankali sosai kan girmamar juna, da goyon bayan juna, da inganta hadin gwiwa, don samun ci gaba tare.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China