Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 70 da cimma nasara kan yakin duniya na biyu, kasar Rasha za ta gudanar da bukukuwa da dama a wannan shekara domin tunawa da babbar nasarar da sojojin Soviet suka samu wajen yakin kare kasa.
A ran 6 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi shawarwari da wakilan 'yan mazan jiya da suka halarci yakin duniya na biyu a birnin Staraya Russa. Kuma a yayin da suka tsokaci kan yadda za a iya dakatar da laifuffukan dake shafar canja tarihin yakin duniya na biyu, Mr. Putin ya bayyana cewa, ko da a halin yanzu, akwai wasu mutanen dake son yin amfani da karfin siyasa domin canja tarihi, kamar mai da 'yan Nazi a matsayin jarumai, amma hakan ba zai cimma ruwa ba, sabo da yanayin siyasa ba zai iya canja tarihi ba, kuma neman yin hakan zai iyar haddasa illa ga zaman takewar al'umma, kuma abin mafi tsanani shi ne, rage rigakafin da jama'ar kasa da kasa za su yi kan yaki da masu tsattauran ra'ayi da kuma tsarin jagoranci na Nazism. Kuma ko shakka babu, babu wanda zai iya canja tarihi. (Maryam)