Yayin ganawar tasu, shugaba Putin ya bayyana cewa dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin ta kai matsayin koli a tarihi, kana hadin gwiwarsu ya dace da bukatunsu na yanzu, da ma na nan gaba.
Ya ce kasar Rasha ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da moriyarta, da nuna goyon baya ga kafa zirin tattalin arziki na hanyar siliki, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da biyu da suka gabata, shugaba Xi Jinping da shugaba Putin sun tsara shirin raya dangantakar dake tsakanin kasashen su, bisa bunkasuwar kasashen biyu, da halin zaman lafiya da bunkasuwar duniya. Kaza lika suna ci gaba da himma wajen raya dangantakar abokantakarsu a dukkan fannoni. (Zainab)