An bada labarin cewa tuni sashen birnin Moscow na ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Rasha suka yi bincike a wurin da lamarin ya faru.
Sakataren watsa labaru na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya bayyana cewa, shugaba Vlładimir Putin ya yi nuni da cewa, bisa alamar da aka samu, an tsara shirin kai hari ga Nemtsov ne, wanda ya zama tsokana. Tuni shugaba Putin ya riga ya bada umurnin fara bincike, tare da jiran sakamakon kai tsaye. Daga nan, sai shugaba Putin ya nuna ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan Nemtsov.
A ranar 1 ga watan Maris, kungiyar adawa ta kasar Rasha za ta yi zanga-zanga don nuna adawa ga gwamnatin kasar a kan shiga rikicin gabashin kasar Ukraine, tare da ta zargi gwamnatin a kan manufofin da ta gabatar da suka sanya tattalin arzikin kasar ya fuskanci matsala. Nemtsov yana daya daga cikin mutanen da suka yi kira da yin zanga-zangar. (Zainab)