in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar gwamnatin kasar Jamus ta sake jaddada anniyar yin hadin gwiwa da Rasha kan gina tsaron Turai
2015-02-08 17:11:41 cri
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana a ranar jiya 7 ga wata a yayin taron tsaro na Munich cewa, kasar Jamus tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Rasha domin gina tsaron Turai.

A cewarta, rabuwar kasashen Turai za ta haddasa illa ga moriyar dukkanin mutanen yankin, kasar Jamus ba ta son ganin haka, tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Rasha domin gina tsaron Turai tare, a maimakon nuna kiyaya ga kasar Rasha.

Haka kuma, a yayin da take tsokaci kan tattaunawar shugabannin kasashen Jamus, Rasha da Faransa kan batun kasar Ukraine da suka gudanar a birnin Moscow na kasar Rasha a ran 6 ga wata, madam Merkel ta bayyana cewa, a halin yanzu, ba za a iya tabbatar da cimma nasarar shawarwarin ba, amma ya kamata bangarorin da abin ya shafa su ci gaba da dukufa kan aikin.

A ran 6 ga wata, shugabannin kasashen uku da suka hada da Angela Merkel, Francois Hollande da kuma Vladimir Putin sun yi ganawa a birnin Moscow domin tattaunawa kan hanyoyin warware rikicin Ukraine, kuma bisa labarin da kasar Rasha ta fitar bayan tattaunawar, an ce, mahalarta taron suna shirya fitar da wani daftarin gudanarwa na yarjejeniyar Mensk, ciki hada da shawarar da shugaban Ukraine da shugaban Rasha suka bayar, kana za a gabatar da darfarin nan ga dukkanin bangarorin da rikicin kasar Ukraine ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China