Gwamnatin kasar Rasha ta amince da jam'iyyar adawa da ta shirya zanga-zangar nuna ta'aziyya a birnin Moscow a yau ranar Lahadi 1 ga watan Maris, wanda za a fara da karfe 3 da yamma bisa agogon wurin, kana hanyoyin zanga-zanga sun hada da wurin da aka harbe Boris Nemtsov, da wasu wuraren dake kewayen wurin, amma bai kamata adadin masu zanga-zanga ya zarce sama da dubu 50 ba, bugu da kari, rundunar 'yan sanda ta birnin Moscow ta bayyana cewa, za ta dauki matakan da suka dace domin fuskantar harkokin gaggawa da mai iyuwa ne za su faru a yayin zanga-zangar.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a ran 28 ga wata cewa, hukumomin kasar da abin ya shafa za su dukufa domin gurfanar da wadanda suka shirya da aikata kisan Boris Nemtsov. (Maryam)