Da yake tsokaci game da hakan, babban kwamandan askarawan sojin kasar ta Rasha Valery Gerasimov, ya ce kasarsa za ta tabbatar da kasancewa cikin damara, ta fuskar makamanta na nukiliya, da kuma karfin sojin.
Gerasimov ya ce jibge karin na'urorin kakkabo makaman nukiliya da Amurka ke yi a yankunan Asia da Fasifik, daya ne daga dalilan da ya sanya Rashan daukar nata matakai.
A nasa bangare ministan tsaron kasar ta Rasha Sergei Shoigu, jaddada wannan aniya ya yi, yana mai cewa rundunar sojin kasarsa ta himmatu, wajen zartas da wannan sabon kudurin tsaro bisa umarnin shugaba Vladimir Putin.
Shoigu ya kara da cewa Rasha za ta fadada tsarin tsaronta na shekarar 2016 zuwa 2020, kafin gabatar da shi ga shugaba Putin domin neman amincewarsa nan da watan Disambar karshen wannan shekara.
Ya ce tsarin ya tanaji daukar matakan daga matsayin karfin sojin kasar, tare da hadin gwiwa da sauran sassan gwamnatin kasar, wajen karfafa ikon Rashan na fuskantar sabbin kalubalen tsaro. (Saminu Hassan)