in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta karbi shugabancin kungiyar kasashen BRICS na shekarar 2015
2015-01-02 16:23:25 cri

Tun daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2015 da muke ciki, kasar Rasha ta kasance mai shugabancin kungiyar kasashen BRICS na wannan shekara. Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce, kasarsa za ta yi amfani da wannan dama domin kara inganta tasirin da kasashen BRICS suke bayarwa a fadin duniya.

A sakon murnar sabuwar shekara da shugaba Putin ya aika zuwa ga takwararsa madam Dilma Rousseff ta kasar Brazil, ya yi nuni da cewa, tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS wato kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu ya samu sakamako mai kyau a fannonin kara azama kan samar da kayayyakin masana'antu da yin mu'amalar fasaha, haka kuma yana taimakawa kwarai da gaske wajen yin mu'amala a tsakanin kasashen 5 a fannonin kiwon lafiya, ba da ilmi, kimiyya da makamantansu

Har wa yau matsayin da kasashen BRICS suke tsayawa a kai a fannin tabbatar da tsaro a tsakanin kasa da kasa da kuma bayanai daya ne, don haka akwai sa ran yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Haka kuma, kasashen 5 za su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin makamashi, sarrafa amfanin gona na zamani da dai sauransu.

A farkon watan Yuli na wannan shekara ne za a gudanar da taron kolin kasashen na BRICS a birnin Ufa dake kasar Rasha. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China