Bayan ganawarsa da ministan harkokin waje na Birtaniya Philip Hammond, a ranar Asabar din nan a birnin Landan, John Kerry ya bayyana cewa, a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, shugaba Obama zai yi la'akari da matakan da za a dauka, daga bisani, a san me za'a yi a nan gaba. Wadannan matakai sun hada da ko za a bayar da makamai ga sojojin Ukraine ko a'a, da kuma kara sanya takunkumi ga Rasha sabo da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tayi.(Fatima)