Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Burundi ya ce wasu hare-hare biyu da aka kai kan wasu cibiyoyin bincike na 'yan sanda, a birnin Bujumbura hedkwatar kasar Burundi a ranar Juma'a, sun haddasa mutuwar 'yan sanda biyu, da kuma farar hula daya, yayin da wasu 17 suka samu raunuka.
Yayin wani taron manema labaru da aka gudanar a jiya Asabar, rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana cewa, hare-hare biyu sun auku ne kusan a lokaci guda, daya daga cikinsu a arewacin birnin na Bujumbura, kuma wasu mutane biyar ne da ba a tantance da su ba suka jefa nakiyoyi biyu ga cibiyar binciken ta 'yan sanda. Yayin da daya harin kuma ya auku a kusa da wata kasuwa dake cibiyar birnin, lamarin da janyo jikkatar 'yan sanda biyar, ciki hadda 3 da suka samu munanan raunuka. (Amina)