Ruwan saman na ranar Litinin 10 ga wata, acewar masu aikin jiyya na kungiyar agaji ta Red Cross, na hade da iska mai karfi, wadda ta kwaye rufin gidaje da dama, lamarin da ya sa mutane da yawa ji raunuka. Red Cross ta kuma ce idan har ruwan bai tsagaita ba a 'yan kwanakin nan, karin gidaje masu yawa za su lalace.
Bugu da kari rahotanni sun bayyana cewa, iskar ta kwashe rufin dakuna hudu, a wata makarantar midil dake Gatumba, wanda hakan ya sanya aka dakatar da wasu darussa a makarantar. Ya zuwa yanzu dai mutane kimanin 1000 ne suka rasa gidajen su a wannan yanki.
Bisa kiyasin da ofishin nazarin yanayin kasar ya bayar, an ce cikin watanni biyu masu zuwa, za a fuskanci ruwan sama mai tarin yawa a yawancin sassan kasar.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 9 ga watan Fabrairun bana ma, wasu yankuna dake arewacin birnin na Bujumbura, sun sha fama da ruwan sama mai karfi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 75, yayin da kuma wasu gidaje da dama suka rushe. (Amina)