A wannan rana, Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya ce, kwanan bayan, da jam'iyya mai mulki ta Burundi ta tabbatar da shugaba mai ci yanzu Pierre Nkurunziza a matsayin dan takarar jam'iyyar, an samu tashe-tashen hankali a kasar.
A don haka Mr Ban Ki-moon ya yi Allah-wadai da lamarin, kuma ya bukaci gwamnatin Burundi da ta yi bincike kan tashe-tashen hankalin.
Yana mai bayanin cewa, ya tura Said Djinnit zuwa Burundi don yin shawarwari da Pierre Nkurunziza da sauran shugabannin jam'iyyun siyasar kasar. Ya kuma bukaci bangarorin da abin ya shafa da su dakile tashe-tashen hankali, da magance zugar mutane don ta da tsaune-tsaye. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga al'ummar Burundi da su warware rikici ta hanyar yin shawarwari, da sake nanata matsayin da MDD take tsayawa don yin zaben gaskiya cikin adalci da lumana.(Bako)