Kaza lika Mr. Ban ya kuma yi fatan gudanar da babban zaben kasar Burundin nan gaba cikin wannan sabuwar shekara, cikin kyakkyawan yanayin zaman lafiya da lumana.
Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, bisa kudurin kwamitin sulhun MDD game da wannan batu, tawagar sa idon ta MDD a kasar Burundi,ta riga ta fara gudanar da ayyukanta a hukumce tun daga ranar 1 ga watan nan na Janairu, aikin da manzon musamman na babban magatakardar MDD Cassam Uteem daga kasar Mauritius ke jagoranta.
Har ila yau ana sa ran tawagar za ta binciki, ta kuma gabatar da yanayin gudanar da zaben shugaban kasar, da na majalisar dokoki, da kuma zaben kananan hukumomin kasar dake tafe daga watan Mayu zuwa watan Satumbar wannan shekara.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, gudanar da babban zaben kasar ta Burundi cikin yanayin zaman lafiya, da amincewar jama'ar kasar na da muhimmiyar ma'ana ga al'ummar Burundi, ana kuma sa ran kasar za ta yi amfani da wannan dama yadda ya kamata, domin karfafa zaman lafiya da lumana a kasar.
A watan Fabarairun shekarar 2014 ne dai kwamitin sulhun MDD, ya zartas da kudurin da ya bukaci babban magatakardar MDD, ya aike da wata tawagar sa ido ga babban zaben kasar ta Burundi, domin lura da kuma gabatar da bayanin yadda babban zaben kasar na shekarar 2015 zai gudana. (Maryam)