Manyan kusoshin jam'iyyar CNDD-FDD mai mulkin kasar ne suka tabbatar da amincewarsu, da takarar shugaban mai ci, yayin babban taron jam'iyyar da ya gabata a jiya Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa baya ga jiga-jigan jam'iyyar mai mulki, jami'an diflomasiyyar kasar, da wakilan ragowar jam'iyyun siyasa, tare da wakilan jam'iyyun gama kai na kasar sun halarci taro.
Bayanai da suka fito daga taron sun nuna cewa shugaban mai ci ne ya lashe dukkanin kuri'un da aka kada na neman tsayawa takarar, wanda hakan ke nuna cewa ragowar wadanda a da suka nuna burinsu na tsayawa takarar sun janye ke nan.
Bayan bayyana wannan sakamako, shugaban jam'iyyar CNDD-FDD Pascal Nyabenda, ya ja kunnen al'ummar kasar da su kaucewa gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da hakan, domin a cewar sa hakan ya sabawa dokar kasar. Daga nan sai ya yi kira ga jami'an tsaron kasar, da su tabbatar da ci gaba da kare doka da oda.
A nasa bangare shugaba Nkurunziza, bayyana godiyarsa ya yi ga wannan amincewa da ya samu, yana mai alkawarta gudanar da sahihin zabe, ba tare da la'akari da duk wata jita-jita da ka iya shafar burin nasa ba. (Saminu Hassan)