Kwamitin mai mambobi 15 wanda ya bayyana haka a jiya cikin wata sanarwar shugaba da aka raba wa manema labarai bayan zaman da ya yi kan kasar ta Burudi, ya kuma yi maraba da irin ci gaban da aka samu a kasar tun bayan da aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Arusha a shekarar 2000, musamman mai do da tsaro da zaman lafiya a kasar.
Kwamitin ya kuma bayyana cewa,yarjejeniyar ta Arusha ta taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya na tsawon shekaru a kasar Burundi.
Bugu da kari a cewar sanarwar, kwamitin na maraba da ci gaban hadin gwiwar abokan huldan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ciki har da kungiyar AU don goyon bayan shirin yin kwaskwarima da harkokin zabe a kasar.
Wani muhimmin abu game da zabukan kasar ta Burundi na wannan shekara shi ne, 'yan kallon MDD ne za su sa-ido kan zaben kasar ta yadda zai dace da kudurin kwamitin sulhun.
A ranar 26 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaben larduna da na 'yan majalisun dokoki, yayin da za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 26 ga watan Yuni kana zaben 'yan majalisun dattawa ya biyo baya a ranar 24 ga watan Agusta.(Ibrahim)