in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da takwaransa na Burundi
2014-08-16 16:47:14 cri
Yau Asabar 16 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza a birnin Nanjing dake kasar Sin.

A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya nuna matukar maraba ga zuwan shugaba Nkurunziza a birnin Nanjing, don halartar gasar wasannin Olympics ta matasa. Haka kuma, Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu kan ayyukan noma, samar da wutar lantarki da ruwa da kuma gina kayayyakin more rayuwa da dai sauransu, ta yadda za a iya taimaka wa kasar Burundi wajen raya tattalin arziki. Haka kuma da samar da karin guraben aikin yi, kyautata zaman rayuwar jama'a, tabbatar da samar da isashen abinci a kasar da dai sauransu. Kaza lika, ya kamata a ci gaba da yin musayar al'adu a tsakanin kasashen biyu, Sin tana goyon bayan Burundi wajen kiyaye zama lafiya da tsaron nahiyar Afirka.

A nasa bangaren kuma, shugaban kasar Burundi Mr. Nkurunziza ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka waje nuna goyon baya ga kasar Sin da ta kiyaye ikon mulkinta da kuma cikakken yankunanta, kuma tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako ga kasar Budundi wajen kyautata kayayyakin more rayuwa a kasar, habaka gina ayyukan makamashi, ba da ilmi da harkokin kimiyya da fasaha da dai sauransu, kaza lika, tana maraba da karin zuba jari daga kasar Sin, kasar Burundi za ta ci gaba da halartar ayyukan kiyaye zaman lafiyar Afirka, kuma tana fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a wannan fanni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China