Ranar 17 ga wata da dare, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa, inda ya bayyana yiwuwar abkuwar tashin hankali a kasar Burundi sakamakon gudanar da zabuka nan gaba ba da dadewa ba, ya kuma kalubalanci sassa daban daban na kasar da su tabbatar da gudanar da zabuka cikin zaman lafiya ba tare da rufa-rufa ba, da kuma sassa daban daban za su shiga.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhu na ganin cewa, zabukan da za a gudanar a Burundi a wata mai zuwa za su jawo hankali matuka, wadanda kuma za su iya haifar da tashin hankali, lamarin da zai iya lalata zaman lafiyar da ke kasar cikin kusan shekaru 10. Don haka kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar da su kiyaye zaman lafiya a kasarsu, bayan sun jurewa wahalhalu. Kana kuma kwamitin sulhun ya jaddada cewa, kamata ya yi gwamnatin Burundi da 'yan adawa su yi kokarin magance ko wane irin tashin hankali ko barazana, ta yadda za su yi kokarin goyon bayan samar da kyawawan sharudan gudanar da zabukan yadda ya kamata.
Za a gudanar da zabukan 'yan majalisu a ranar 26 ga watan Mayun bana, yayin da shugaban kasa a ranar 26 ga watan Yuni. Kungiyar sa ido kan zabukan Burundin a karkashin shugabancin MDD ta soma aikinta a watan Janairun bana, wadda za ta sa ido da kuma mika rahoto kan yadda za a gudanar da zabuka a Burundin. (Tasallah Yuan)