in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi zai kawo ziyarar aiki a kasar Sin
2014-08-15 09:59:44 cri
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunzizia ya bar birnin Bujumbura a ranar Alhamis da yamma zuwa kasar Sin, inda zai kawo ziyarar aiki daga ranar 14 zuwa 19 ga watan Agusta.

A cewar wata sanarwar da ta fito daga ofishin watsa labarai na fadar shugaban kasa, mista Nkurunzizia zai gana da manyan shugabannin kasar Sin, shugabannin kamfanonin Sin da kuma daliban Burundi dake karutu a kasar Sin.

Haka kuma, shugaba Nkurunzizia zai je Nanjing, birnin dake gabashin kasar Sin, inda zai ziyarci wata makarantar wasannin motsa jiki ta Nanjing. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China