Ina ba da lokaci nan da wannan ranar Jumma'a 21 ga watan Maris na shekarar 2014, kana muna fatan wadanda ba su amince da wannan ko wani mataki ba, to za su iya canja ra'ayoyinsu a yayin zaman taron majalisa, sannan kuma su kada kuri'a kan wasu kudurori da muka gabatar cikin jadawalin taron, in ji mista Nduwuburundi.
Jam'iyyar CNDD FDD na da 'yan majalisu 81 cikin 106 da majalisar dokokin kasar take kunshe da su, a yayin take bukatar 'yan majalisu 85 domin shigar da wannan sabon kundin tsarin mulki da aka ma gyaran fuska. (Maman Ada)