Mambobin kwamitin tsaron sun kuma yi tir da duk wani mataki, da ka iya haifar da tayar da hankula ko hargitsi a kasar, biyowa bayan zargin da ake yi cewa, akwai alamun tirsasawa, ko keta hakkokin al'umma da tsagerun matasa ke yi a kasar.
Har wa yau kwamitin tsaron ya yi kira ga mahukuntan kasar, da su dauki matakan magance aukuwar laifuka masu alaka da cin zarafin al'umma ko 'yan adawa, su kuma tabbatar da kiyaye doka da oda. Matakan da za su baiwa daukacin jam'iyyun kasar damar shiga a dama da su yadda ya kamata, yayin babban zaben kasar.
A watan Fabarairun da ya shude ne dai aka tsare jagororin jam'iyyar adawa ta Uprona, matakin da ya haifar da barazana, ga kokarin da ake yi na dinke Barakar dake akwai, tsakanin 'yan kabilar Hutu masu rinjaye, da tsirarun 'yan kabilar Tutsi.
Har wa yau zaman dar dar ya kara tsananta, bayan arangamar da dakarun sassan biyu suka yi da jami'an 'yan sanda a ranar 8 ga watan Maris.
Kasar Burundi dai na shan fama da rigingimu masu alaka da kabilanci, wadanda kan kai ga kasha-kashe, da yakin basasa. (Saminu Alhassan)