in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya nuna damuwarsa game da fito na fito tsakanin 'yan adawa da 'yan sanda a Burundi
2014-03-14 10:45:26 cri
Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Alhamis din nan 13 ga wata ya nuna matukar damuwar shi game da mummunan fito na fito da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan adawa a kasar Burundi makon da ya gabata. Yana mai kira ga bangarorin gwamnati da na 'yan adawan da su kai zuciya nesa su guji aikata duk wani abin da zai dagula halin fargaban da ake cikin a yanzu.

Mr Ban ya koka a kan dokar da ta takura 'yancin fadin albarkacin bakinka da taron na jama'a ko kungiya musamman dokar da ta ba da damar a tarwatsa taron 'yan adawa ko a ma hana su taruwa gaba daya da 'yan sanda suka yi ma 'yan adawan reshen matasa, in ji sanarwar da Kakakin MDD ya fitar.

Mr Ban ya ce mutunta wadannan dokoki na 'yan ci da sauran dama na walwalar jama'a wasu ka'idoji ne dake cikin gudanar da babban zabe mai zuwa cikin adalci da gaskiya kuma kasar bai kamata ta yi sake da wannan dama ba na cin gajiyar mulkin demokradiya.

Babban magatakardar ya kara ma gwamnatin kasar ta Burundi, shugabannin 'yan siyasa da na kungiyoyi kwarin gwiwa na su yi aiki tare domin rage fargaban da ake ciki yanzu haka, in ji sanarwar wadda ta ba da tabbacin goyon bayan majalissar wajen ganin hakan ya tabbata.

Mr Ban Ki-Moon ya kuma jaddada kiran shi ga gwamnatin Burundi da shugabannin jam'iyun siyasa da suke aiwatar da shirin wayar da kan jama'a a kan su guji ayyukan tashin hankali a lokacin zaben dake tafe, sannan su warware bambancin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari kamar yadda tsarin dokar zaben kasar da aka fitar a bara ta amince da shi da kuma tanadin dake cikin yarjejeniyar Arusha. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China