MDD, ta hanyar tawagar sa ido kan zabe wanda nan da dan lokaci za ta iso Burundi, haka kuma ta hanyar Equipe/Pays, za su karfafa aikin taimakawa Burundi ta hanyar kasancewar abokin hulda mai muhimmaci ga kasar Burundi, in ji mista Feltman a yayin wani taron manema labarai bayan rufe kofar cibiyar BNUB a kasar Burundi.
A wannan lokaci da kasar Burundi take shirye-shiryen gudanar da zabubukanta karo na uku bisa tsarin demokaradiya tun bayan kawo karshen yakin basasa, MDD za ta ci gaba da kasancewa kusa da 'yan kasar Burundi a duk tsawon lokacin zabe tare da tawagar aikin zabe ta MDD game da kasar Burundi (MENUB) da za'a tura a ranar daya ga watan Janairun shekrar 2015, in ji mista Feltman.
A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Burundi, Laurent Kavakure, ya yi amfani da wannan dama domin isar da godiya ga MDD kan babban taimakon da ta bayar wajen gudanar da muhimman ayyuka a kasar Burundi. (Maman Ada)