in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Jami'an tsaro sun dakile wani yunkuri na fasa gidan yari
2015-02-21 16:54:02 cri

Rundunar 'yan sanda a tarayyar Najeriya, ta ce jami'anta sun samu nasarar dakile wani yunkuri na fasa gidan yarin Afokang dake birnin Calaban jihar Cross River.

A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar Horgan Bassey, wasu mahara da ba a tantance ko su waye ba ne suka farma gidan yarin na Afokang, sai da a cewar sa hakar su bata cimma ruwa ba. Bassey ya ce jami'an tsaro sun samu nasarar dakile yunkurin fasa gidan yarin.

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka yayin dauki ba dadin da jami'an tsaro suka yi da maharan ba, kana ya ce za a gudanar da bincike game da aukuwar lamarin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China