in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kira ga kasar Togo da ta gudanar da babban zabe cikin lumana
2015-04-25 16:59:11 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon, ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, wadda ke kira ga sassa daban daban na kasar Togo da su tabbatar da an gudanar da zaben shugabancin kasar dake tafe cikin lumana, da 'yanci, ba kuma tare da wata rufa-rufa ba.

Sanarwar kuma ta yi kira ga shugabannin kasar da mabiyansu, da su warware matsalolin da ka iya bullowa yayin zaben bisa tsarin mulkin kasar. Ban da haka Ban Ki-Moon ya nanata cewa, MDD na goyon bayan aikin share fagen gudanar zaben, da kuma kokarin da jama'ar kasar ke yi na kiyaye dimokuradiyyar kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China