Sabuwar gwamnatin na kunshe da mambobi 27, cikinsu,har da tsohon mai ba da shawara ga shugaban Faure ta fuskar diplomasiyya Robert Diesel wanda ya zama ministan harkokin wajen kasar, yayin da wani tsohon mai ba da shawara ga shugaban ta fuskar diplomasiyya na daban Kofi Esaw ya rike mukamin ministan shari'a da hukumomin kasar. Haka kuma, tsohon ministan harkokin wajen kasar Elliott OHIN ya zama ministan kula da tsare-tsaren samun ci gaba.
A ranar 25 ga watan Yuli na bana ne, aka yi zaben majalisar dokoki a kasar Togo,inda jam'iyyar hadin gwiwa don kiyaye jamhuriyar Togo da ke karkashin shugabancin Faure, ta samu kujeru 62 cikin kujeru 91 a majalisar dokokin kasar. A ranar 6 ga wata, Faure ya ba da umurnin sake nada Ahoomey-Zunu a matsayin firaministan kasar, kuma ya bukace shi da ya kafa sabuwar gwamnati.(Bako)