in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage zaben shugaban kasar Togo zuwa 25 ga watan Afrilu
2015-03-29 15:38:53 cri
Gwamnatin kasar Togo ta sanar a ranar Asabar da matakin dage zaben shugaban kasar na ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 25 ga watan Afrilu.

Taron ministoci na ranar Jumma'a ya dauki wannan mataki ta yin la'akari da bukatun da shugaban kungiyar ci gaban tattalin kasashen yammacin Afrika ECOWAS mai ci yanzu wato shugaban kasar Ghana John Hahama Dramani ya gabatar a karshen wata ziyarar aiki a ranar 24 ga watan Maris, a yayin shawarwarin da ya yi tare da hukumomin kasar Togo, 'yan takarar zaben shugaban kasa da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI, a cewar wata sanarwa da gwamnatin kasar Togo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China