Shugabannin kasashen biyu, da ake tsammanin zuwansu a safiyar yau Talata a babban birnin Niamey, za su tattauna tare da takwaransu na kasar Nijar, Issoufou Mahamadou a fadar shugaban kasar a cewar wannan majiya.
Kafin daga baya, shugabannin su shirya wani taron manema labarai domin mai da hankali ga dukkan alamu kan batutuwan huldar dangantaka da tsaro a cikin shiyyarsu musammun ma kan yaki da kungiyar Boko Haram da ke gudanar da ayyukanta na ta'addanci a yankin tafkin Chadi.
Kasashen Benin, Mali da Faransa dai, sun aike a makon da ya gabata da wasu manzanninsu domin kawo goyon baya ga shugaba Mahamadou Issoufou, tare da mika masa wasikun nuna jimami, goyon baya da tallafinsu bayan hare haren da wannan kungiyar ta'addanci ta kai a kasar Nijar. (Maman Ada)