Da safiyar wannan rana ne jami'an kiwon lafiyar su 3, da aka tura daga lardin Shanxi na kasar Sin suka gabatar da jawabi ga likitoci 30, dake kwalejin kiwon lafiyar kasar, game da alamun kamuwa da cutar Ebola, da fasahohin da Sin ke bi wajen yaki da cututtuka masu yaduwa, da manufofin rigakafi, da yaki da cutar Ebola da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gabatar da dai sauransu.
Kaza lika jami'an lafiyar kasar Togo sun gwada dabarun amfani da rigunan kariya da suka koya, sun kuma gabatar da tambayoyi ga kwararrun na Sin game da rigakafi da yaki da cutar Ebola.
Wani jami'in ma'aikatar harkokin kiwon lafiyar kasar ta Togo ya gabatar da godiyar su ga gwamnatin kasar Sin, game da horon. Ya ce, horon ya kunshi fannoni daban daban, zai kuma taimaka wajen kara ikon likitocin kasar Togon a fannin rigakafi da yaki da cutar Ebola. (Zainab)