Wannan rancen kudi na bankin BOAD ya cimma Sefa biliyan 43 na jimillar adadin ayyukan da bankin yake kan tashar ruwan birnin Lome.
Ayyukan sun shafi sake gina hanyoyi da filayen zirga zirga da suka tsufa a cikin tashar ruwan, gani wani tsarin tsabtacewa, sake gina da fadada tasrin samar da ruwa masu tsabta, gyara tsarin layoyin wutar lantarki da na wayar tarho, fadada manyan hanyoyi, gina wuraren fakin, da gina hanyoyin shiga da fita.
Wadannan ayyuka za su taimaka wa tashar ruwan Lome kara karfin yin takara, kamar irin tashoshin ruwan kasa da kasa, haka kuma zai kara taimkawa wajen harkokin shige da fice daga kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, da ayyukan shige da fice daga wadannan kasashe ya wuce fide kashi 20 cikin 100, in ji shugaban bankin BOAD. (Maman Ada)