Tuni dai aka gudanar da bikin bayar da kayayyakin a cibiyar bada gudummawa ta kasar Togon, wanda ya samu halartar ministan kula da harkokin zamantakewar al'umma da harkokin mata, da kawar da jahilci na kasar Dédé Ahoéfa Ekoué, da jakadan Sin dake kasar Togo Liu Yuxi.
Kayayyakin da aka bayar dai sun hada da na'urorin amfani na yau da kullum, da kayayyayin wasannin motsa jiki da al'adu, da kayan abinci, da kayayyakin wasa da dai sauransu, wadanda za a mika su ga kananan yara marayu, ko masu fama da talauci fiye da 5200 a yankuna 36 dake kasar.
Cikin jawabinsa yayin bikin, Mr. Ekoue ya jinjinawa kungiyar Sinawa mazauna Togo da ofishin jakadancin Sin dake kasar, bisa tattara wannan gudummawa, kana ya bayyana cewa, yawan kudin da kasar Sin ta baiwa cibiyar bada gudummawa ta kasar Togo ya dara na sauran kasashen duniya. (Zainab)