Ana sa ran za a kashe kudi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 1500 kan wannan aiki da aka fara gudanar da shi a watan Disamba na shekarar 2011 kudin da aka samu sakamakon shirin samar da rancen kudi mai gatanci daga bankin The Export-Import Bank of China bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Haka kuma ana sa ran za a kammala aikin a ranar 15 ga watan Agusta na shekara mai zuwa. Bayan kamala aikin filin jiragen sama zai iya yin jigilar fasinjoji daga dubu 400 zuwa dubu 2000 a ko wace shekara, sannan yawan kayayyakin da zai iya jigilar zai karu daga ton dubu 10 zuwa dubu 50 ko wace shekara.