Jami'in ya yi wannan furuci ne a lokacin wani taron manema labarai bayan ya kammala wani rangadin aiki na yini daya a ranar Laraba a Lome, babban birnin kasar Togo.
Mista Djinnit ya ce, "ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki domin ganin an gudanar da wannan zabe cikin zaman lafiya. Domin zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro su ne jiga-jigan abubuwan dake da muhimmancin gaske ga ci gaban kasashenmu."
Haka zalika jami'in ya bukaci jam'iyyun siyasa da su yi kokarin kaucewa duk wasu kiraye-kiraye da za su iyar janyo sabani ko tashe-tashen hankali.
Baya ga haka mista Djinnit ya bayyana muhimmancin kawo gyare-gyaren tsarin mulki da na hukumomi, ta yadda kasar Togo za ta tanadi wani tsarin mulki da zai samu amincewar kowa domin tallafawa zaman lafiya da samun ci gaba. (Maman Ada)