in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar da shugaban Togo ke ciki ta samu kashi 2 cikin kashi 3 na kujerun majalisar dokokin kasa
2013-07-29 15:06:05 cri
Ran Lahadi 28 ga wata da dare, ta Gidan Talabijin din kasar Togo, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta sanar da sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a ran 25 ga wata. Kuma bisa sakamakon da ta bayar, jam'iyyar "the Union for the Republic" da shugaban kasar Faure Essozimna Gnassingbe ya kafa a watan Afrilu na shekarar 2012 ta samu kujeru guda 62 cikin sabbin majalisar dokokin kasa wanda gaba daya ke hada da kujeru guda 91.

Mai kula da harkokin hukumar zabe mai zaman kanta ya bayyana cewa, an gudanar da harkokin zaben cikin yanayin zaman lafiya tare da kuma cimma alkawaran 'yancin kai da ba a boye kome ba da hukumar ta bayar.

Bugu da kari, hukumar za ta gabatar da sakamakon farkon nan ga kotun tsarin mulki don yin bincike kan sakamakon, sa'an nan kuma, koton zai sanar da sakamakon karshe bayan 'yan kwanaki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China