'Yan takara guda 1174, daga jam'iyyoyi da kungiyoyin siyasa guda 8, da suka hada da kawancen hadin kan jama'ar kasar Togo dake kan gadon mulki da dai sauran jam'iyyu suna fafutukar neman kujeru guda 91 na majalisar dokokin kasa.
Shugaba Faure Essozimna Gnassingbe da kuma firaminista Ahoomey Zunu na kasar Togo sun kada kuri'unsu a wannan rana da safe, kana an kammala jefa kuri'a ran 25 da karfe 4 na yamma.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar zata sanar da sakamakon farko na zaben cikin a daren wannan rana. Kungiyar tarayyar kasashen Afirka da kuma gamayyar tattalin arzikin yammacin kasashen Afirka da dai sauran kungiyoyin sun tura masu sa ido kan zaben.
A baya dai an tsai da kudurin gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Togo a watan Oktoba na shekarar 2012, to amma an jinkirtar da hakan saboda bambancin ra'ayi kan harkokin zabe, tsakanin gwamnati da jam'iyyar dake adawa ta kasar. (Maryam)