in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kamfanin kasar Sin ya kaddamar da shirin taimakawa daliban kasar Togo da tallafin kudin karatu
2015-03-31 16:37:18 cri
A ranar Litinin, kamfanin China Merchants Group na Sin ya kaddamar da wani shirin taimakawa daliban kasar Togo da tallafin kudin karatu a birnin Lome hedkwatar kasar.

Jakadan Sin dake kasar Togo Liu Yuxi da ministan kula da ilmi da kimiyya da fasaha na kasar Togo Octave Nicoué Broohm sun halarci bikin kaddamar da shirin da aka yi a wannan rana.

Babban manajan kamfanin Li Xiaopeng ya ce, bisa tsarin tallafin kudin karatu da kamfaninsa da jami'ar Lome suka kafa tare, kamfanin zai biya kudin da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 200, don yaba wa nagartattun dalibai a jami'ar.

A nasa bangare kuma, Octave ya jinjina ma kamfanin da ya kafa wannan tsari a kasarsa, kuma yana ganin kamfanin ya dauki wannan mataki cike da hangen nesa. Ya ce, yayin da kamfanonin kasar Sin ke ba da taimako wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Togo, sun kuma ba da babbar gudummawa wajen horar da mutane, wannan zai amfana wa matasan wurin. Zuba jari wajen horar da kwararru ya sheda muhimmancin da bangarorin biyu ke dorawa kan raya dangantakar hadin gwiwarsu cikin dogon lokaci.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China