in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bashar al-Assad ya lashe zaben shugaban kasar Sham
2014-06-05 10:52:29 cri

Shugaban majalisar dokokin kasar Sham Jihad Laham jiya ranar 4 ga wata ya sanar da cewa, shugaba mai ci Bashar al-Assad ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka kada a ran 3 ga watan nan.

A cewar Jihad, sakamakon kididdigar kuri'un ya nuna cewa shugaba Bashar ya samu kuri'u miliyan 10 da dubu 32, adadin da ya kai kashi 88.7 cikin dari na yawan kuri'un da aka kada, yayin da Maher Abdul-Hafiz Hajjar ya samu kaso 3.2, sai kuma Hassan al-Nuri da ke da kashi 4.3 cikin dari.

Kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da wani taron sirri da yammacin wannan rana, domin tattauna kan halin da ayyukan jin kai ke ciki a kasar ta Sham, inda aka saurari rahoton da mataimakiyar sakatariya mai kula da harkokin jin kai a MDD Valerie Amos ta gabatar. Bayan taron, Madam Amos ta shelanta manema labaru cewa, watanni 3 ke nan da zartas da kudurin kwamitin tsaron game da baiwa kasar ta Sham taimakon jin kai, amma har ya zuwa yanzu aikin bai samu cikakkiyar nasara ba.

Ya zuwa yanzu dai kashi 7 cikin dari na dukkanin fararen hula, da rikicin kasar ya rutsa da su ne kadai suke iya samu taimako. Ban da haka Amos ta nanata cewa, tawagar ba da tallafin za ta dauki duk wani mataki da ya wajaba domin samar da tallafin jin kai, a yayin da kuma hukumomin MDD, da kungiyoyin ba da tallafi ke matukar bukatar taimakon kudi kasashen duniya don gane da wannan aiki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China