Babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon wanda ke ziyarar aiki a kasar Switzerland, ya ce saboda wakilin majalissar na musamman game da rikicin kasar Sham Lakhdar Brahimi ya yi murabus daga mukaminsa, za a gaggauta nada wanda zai maye gurbinsa, saboda muhimmancin da hakan ke da shi.
Mr. Ban ya bayyana ne a birnin Geneva a ranar 17 ga wata, yana cewa Lakhdar Brahimi yana ci gaba da baiwa MDD shawarwari bayan ya yi murabus.
Har ila yau babban magatakardan MDD ya ce zai tattauna da babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa AL Nabil el-Araby kan wannan mukami.
Ban ya kara da cewa, rikicin kasar ta Sham da aka shafe shekaru 4 ana yi, ya jefa jama'ar kasar cikin mawuyacin hali. Don haka ya dace bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa a shiyyar, da kuma kasashe ko hukumomi wadanda ke da ruwa da tsaki, su yi hadin gwiwa wajen samar da wani shiri na warware rikicin kasar a siyasance. (Amina)