in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sham ta mai da martani game da zargin da EU ta yi kan babban zaben kasar
2014-06-08 20:50:25 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sham ta ce korafin da kungiyar tarayyar turai ta EU ta yi, game da babban zaben kasar ta Sham ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ma burin al'ummar Sham.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a baya bayan nan ta ce, sukar da EU ta yiwa wancan zabe, mataki ne da ya saba wa manufar mutunta ikon mulkin sauran kasashe, da manufar hana tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe.

Kaza lika sanarwar ta ce EU ta furta kalamai da suka sabawa salo irin na dimokaradiyya, wanda ya tanaji baiwa 'yan kasa damar zaba shugaban da suke so. Duba da cewa zaben shugaban kasar ta Sham ko akasin haka, ya ta'allaka ne da burin jama'ar kasa, ba wata kungiya ta daban ba.

Kafin hakan dai babbar wakiliyar EU mai kula da harkokin waje, da manufofin tsaro Madam Catherine Ashton ta bayyana cewa, zaben shugabancin kasar Sham da ya gudana ran 3 ga watan nan ba ya bisa doka, kuma a cewarta, zaben na barazana ga kokarin da ake yi wajen warware rikicin kasar a siyasance. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China