Bisa ajandar da aka tsara, a wannan rana da misali karfe 9 da minti 20, shugabannin kasashen Asiya da Afrika sun taka sayyada daga otel din Savoy Homann zuwa ginin Gedung Merdeka wato inda aka shirya taron Bandung a lokacin baya, wannan tafiya tana da ma'anar tarihi, saboda kafin shekaru 60 da suka wuce, tsoffin shugabannin kasashen Asiya da Afrika sun yi wannan tafiya ce a baya, don halartar taron. A ranar yau, shugabannin kasashen Asiya da Afrika, sun yi tafiyar ne domin tuna da tarihi, da kuma yada akidar hadin gwiwa, sada zumunta da sauransu.
Daga bisani kuma, an yi bikin tunawa da taron Bandung a cikin ginin Gedung Merdeka.
A yayin bikin, shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo, da na kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da na kasar Myama Uhain Sein, da firaministan Masar Ibrahim Mahlab da mataimakin shugaban kasar Venezuela Jorge Arreaza sun yi jawabi daya bayan daya, inda suka bayyana cewa, akwai rashin daidaito da adalci a duniyar da muke ciki, kuma kasashe masu tasowa na ci gaba da fuskantar babban kalubale wajen kare hakkinsu da samun bunkasuwa. A halin da ake ciki yanzu, kasashen Asiya da Afrika na sake taruwa a birnin Bandung, don nazarin akidar taron Bandung, inda suka yi hadin gwiwa da sada zmunta, gami da neman samun bunkasuwa da wadata a tsakanin kasashe masu tasowa, wannan na da ma'anar musamman.(Bako)