in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda shugaba Xi Jinping ya halarci bikin budewar Wasannin Olympics na Sochi nada muhimmancin gaske, in ji jami'in kasar Sin
2014-02-09 16:44:52 cri
Bisa goron gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa, mista Xi Jinping, shugaban kasar Sin, ya kai ziyara a kasar Rasha daga ranar 6 zuwa ta 8 ga watan Fabrairu, don halartar bikin bude wasannin Olympics a lokacin hunturu a birnin Sochi na kasar. Bayan da shugaban kasar Sin ya kammala ziyararsa, ya koma kasar Sin, ministan harkokin wajen kasar mista Wang Yi ya yi bayani kan ziyarar shugaba Xi a gaban manema labarai.

A cewar mista Wang Yi, yayin da jama'ar kasar Sin ke murnar bikin sabuwar shekara na gargajiya, shugabansu mista Xi Jinping ya je Rasha don halartar muhimmin bikin kaddamar da wasannin Olympics na lokacin hunturu. Zuwansa birnin Sochi ke da wuya, shugaba Xi ya fara kokarin ganawa da shugabannin kasashe daban daban, da halartar wasu manyan bukukuwa, bayan ya kammala ayyukan wannan ziyara ya kuma kama hanyarsa ta dawowa gida nan take ba tare da bata lokaci ba. Ziyarar shugaba Xi a wannan karo ita ce ta farko da wani shugaban kasar Sin ya tafi ketare don halartar wani babban bikin wasannin motsa jiki, lamarin da ya sheda kokarin shugabannin kasar Sin a fannin raya harkar diplomasiyya, da mai da hankali kan hakikanan batutuwa.

Ministan ya kara da cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai a birnin Sochi ta nuna yadda kasar Sin take nuna wa kasar Rasha goyon baya a kokarinta na karbar bakuncin wasannin Olympics, kuma ta aza harsashi ga kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2 a shekarar 2014. Kasar Sin da kasar Rasha kawaye ne dake kokarin hadin gwiwarsu a fannin manyan tsare-tsare, in ji mista Wang Yi, don haka bayan da shugaba Xi Jinping ya kama aiki a watan Maris na bara, ya dauki kasar Rasha a matsayin zangonsa na farko na kai ziyara, sannan tare da takwaransa na Rasha mista Putin sun cimma ra'ayi daya kan matakan da za a dauka don zurfafa hadin gwiwar kasashen 2.

Ministan ya kuma kara da cewa, ziyarar shugaba Xi a Sochi ta sheda yadda gwamnatin kasar Sin take dora muhimmanci kan wasannin Olympics. Ya ce, shugaban ya amince da babban ra'ayin wasannin na tabbatar da hadin kai, abokantaka, da zaman lafiya, don haka gwamnatinsa ta yi ta kokarin bunkasa harkar wasannin motsa jiki a kasar ta Sin. Don yaba ma kokarin da shugaba Xi da gwamnatinsa suka yi wajen yada ra'ayin Olympics, kwamitin Olympics ya ba da wata lambar yabo ta musamman ga shugaba Xi Jinping a watan Nuwamban bara, in ji ministan. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China